'Yar wasan kwallon kafa ta musulunta a Sweden

'Yan kasar Sweden wadanda suka yi kaurin suna wajen kyamar Musulmai, sun kadu sosai a sa'ilin  da suka samu labarin musuluntar Ronja Anderson,daya daga cikin kusoshin kungiyarsu ta kwallon kafa ta 'ya 'ya mata,U19.

'Yar wasan kwallon kafa ta musulunta a Sweden

'Yan kasar Sweden wadanda suka yi kaurin sunan wajen kyamar Musulmai, sun kadu sosai a sa'ilin da suka samu labarin musuluntar Ronja Anderson,daya daga cikin kusoshin kungiyarsu ta kwallon kafa ta 'ya 'ya mata,U19.

A wani bayani da ta yi gaban manema labaran daya daga cikin jaridun da aka fi bugawa a Sweden,Afonbladet,Anderson ta ce bayan ta rungumi addinin Musulunci,'yan uwa da aminnan arzikinta sun yi ta cuzguna ma ta tare da jifar ta da kalaman kyama,amma duk da haka tana alfaheri da kasancewa Musulma.

Anderson, kwararriyar mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta 'ya 'ya mata ta IK Uppsala ta kasar Sweden,ta sanar da cewa Musulmantarta ta yi tasiri sosai kan rayuwar kawayenta da dama.

Bugu da kari ta ce,

"Sai bayan na Musulunta, na gane cewa yanzu ne na yi gamdakatar da kyaukyawan addini.Na yi imani da duk abin da Kur'ani ya zo da shi.A yanzu na san Allah,kuma ina ji a jikina irin tallafin da yake mun".

Misiz Anderson wacce a yanzu haka ta shaida cewa tana ci gaba da yin ka-in da na-in wajen ganin ta bi umarnin da Islam ya zo da shi sau da kafa,ta dauki alkwarin azumtar azumin watan Ramalana mai zuwa.

 

 Labarai masu alaka