Bincike: Yawancin 'yan kwallon kafar Afirka na boye ainaihin shekarunsu

A cewar wani rahoto da aka wallafa a baya bayan nan,yawancin masu taka leda na nahiyar bakar fata da ke a manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya sun fesa karya kan ainaihin shekarunsu.

A sanar da cewa wannan lamarin na rage shekaru don samun damar kutsa kai a manyan kungiyoyin kwallon kafa, abu ne da ya zama ruwan dare gama duniya a duk fadin Afirka,inda daga bisani ya fara kunno a Turai.

A jerin dalilan da suka sa 'yan Afirka suka rungumi wannan hanyar don badda kama, akwai matsanancin rayuwa da suke fuskanta a kasashensu na ainahi,talauci, rashin aikin yi, yake-yake, yunwa da kishi da kuncin rayuwa.

Haka zalika an tabbatar da cewa, zai yi wuya 'yan kasashen Afirka masu shekaru 13 suka kara da sa'inninsu na Turai a filin wasan kwallon kafa,saboda ba za su taba yin nasara kansu ba, ganin yadda Turawa suka fi Afirkawa koshi da karfin jiki,wanda hakan ke da nasaba da kyaukyawar rayuwa da kuma lafiyayyen abincin da suke ci,akasin takwarorinsu bakar fata.Labarai masu alaka