'Yar kasar Turkiyya tazo ta daya a gasar tseren fanfalakin Azerbaijan

'Yan kasar Turkiyya mai suna Fadime Çelik ta zo na daya a sashen mata a yayinda dan kasar Turkiyya mai suna Omer Alkanoğlu ya zo na uku a sashen maza a tseren fanfalakin da Kungiyar Haydar Aliyev ta shirya a Baku babban birnin Azerbaijan.

Tseren fanfalakin ya samu halartar mutane dubu 18 da ya fara daga Babban Filin Taron kasar tare da ministan tsaro Edet Guliyev, ministan Ilimi Jayhun Bayramov, Sufuri da Sadarwa Ramin Guluzade, mataimakin shugaban kungiyar Haydar Aliyev Leyla Aliyeva, 'yan majalisu, jakadojin kasashen waje da kuma 'yan wasa.

An dai kammala tseren fanfalakin mai stawon kilomita 21 da ya ratsa gefen teken Hazar zuwa titin Baku a babban filin wasan Baku.

A sashen mata Fadime Çelik ta zo ta daya a yayinda a sashen maza Ömer Alkanoğlu yazo na uku wadanda dukkansu 'yan kasar Turkiyya ne.

A gasar wadanda suka zo na daya zuwa na goma sun samu kaututtukan kudade.

Gasar da aka fara kaddamarwa a shekarar 2016 ya samu halartar yan yawon bude ido daga kasashen waje a inda aka yi amfani da kudaden da aka samu domin tallafawa gajiyayyu.

 Labarai masu alaka