An zargi Ronaldo da yi wa Ba'amurka fyade

Wata 'yar kasar Amurka ta kai karar shahararren dan wasan nan na kasar Portugal,Chistiano Ronaldo ,inda ta ce ya yi ma ta fyade.

An zargi Ronaldo da yi wa Ba'amurka fyade

Wata 'yar kasar Amurka ta kai karar shahararren dan wasan nan na kasar Portugal,Chistiano Ronaldo ,inda ta ce ya yi ma ta fyade.

Matashiyar mai suna Kathryn Mayorga, ta yi hira da maneman labarai gidan jaridan Der Spiegel ta kasar Jamus,inda a nan ne ta fashe kwan.

A cewar Mayorga mai shekaru 34 da haifuwa,dan wasan ya keta ma ta haddi a shekarar 2009 a birnin Las Vegas na Amurka,inda daga bisani ya ba ta na taushiyar baki,zunzurutun kudi yuro dubu 375,000.

Wannan abin kunyar ya bayyana a karo na farko a shekara daya da rabi da ta gabata,amma a lokacin ba a bayyana sunan Kathryn Mayorga ba.

A bara, Ronaldo ya danganta wannan lamarin da "Shafa labari shuni",inda ya tabbatar da cewa ta da yardarta ne suka adu da juna.

Tag: jamus , ronaldo

Labarai masu alaka