UEFA: Galatasaray ta yi rashin nasara a hannun Porto
Kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya Galatasaray ta yi rashin nasara da ci 1 da nema a hannun takwararta ta Porto ta kasar Portugal a wasa na 2 da suka buga a rukunin D na gasar Zakarun Turai ta UEFA.
Kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya Galatasaray ta yi rashin nasara da ci 1 da nema a hannun takwararta ta Porto ta kasar Portugal a wasa na 2 da suka buga a rukunin D na gasar Zakarun Turai ta UEFA.
An buga wasan a filin wasanni na Dragao da ke garin Porto inda aka doke Galatasaray.
A minti na 49 ne dan wasan Porto Marega ya jefa kwallon daya tilo.
Hakan ya sanya Galatasaray zama da maki 3 Porto kuma maki 4.
A daya wasan na rukunin da aka buga Shalke 04 ta doke Lokomotiv Moscow da ci 1 da nema.
A ranar 24 ga Oktoba Galatasaray za ta buga wasanta na 3 da Shalke 04.