Pele ya gargadi Neymar game da Mbappe

Tsohon shararren dan wasan kwallon kafa na kasar Baraziliya Pele ya gargadi dan wasan kasar dake tashe a yanzu mai suna Neymar.

Pele ya gargadi Neymar game da Mbappe

Tsohon shararren dan wasan kwallon kafa na kasar Baraziliya Pele ya gargadi dan wasan kasar dake tashe a yanzu mai suna Neymar.

Pele ya bayyana cewar ba zai kare dan wasan Neymar ba wanda a 'yan kwanakin nan yake zuzuta kansa wanda hakan ya sanya ake sukar sa sosai.

Shahararren dan wasan na Barazil ya ce "Na tattauna da Neymar kuma na fada masa ya yi amfani da dabarunsa a filin wasa. Kar ya ci amanar basirar da yake da ita ta haihuwa da basirarsa ta filin wasa."

Pele ya ci gaba da cewa, Neymar ya fi Mbappe komai da komai, amma kuma a Turai an fi kaunar Mbappe sama da Neymar din.

Pele ya ci gaba da cewar Mbappe yana kama da shi inda ya ce "Tabbas muna kama da juna. Hakan gaske ne. Dukkanmu biyun kafin mu shekara 20 mun halarci gasar cin kofin duniya tare da jefa kwallaye, kuma akarshe muka yi nasara."

 


Tag: Mbappe , Neymar , Pele

Labarai masu alaka