An lallasa Real Madrid a gaban magoya bayanta

A mako na 18 na gasar La Liga ta kasar Spaniya kungiyar Real Sociedad ta doke ta Real Madrid da ci 2 da nema.

An lallasa Real Madrid a gaban magoya bayanta

A mako na 18 na gasar La Liga ta kasar Spaniya kungiyar Real Sociedad ta doke ta Real Madrid da ci 2 da nema.

A wasan da aka buga a filin wasa na Santiago Banabeu real Sociedad ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti 3 da fara wasa inda dan wasata William Jose ya jefa kwallo tare da nasara.

An kammala zagayen farko na wasanna a haka.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci an ba wa danwasan Real Madrid Lucas Vazquez jan kati inda kungiyar ta dawo tana wasa da mutane 10 kawai.

Real Sociedad ta yi amfani da wannan dama inda a aminti na 83 dan wasanta Ruben Pardo ya jefa kwallo 1 a ragar Madrid.

An tashi wasan Real Sociedad na da ci 2 inda Real Madrid take nema.

A yanzu Real Madrid ta sakko zuwa mataki na 5 da maki 30.

Real Sociedad kuma na da maki 22 a gasar.Labarai masu alaka